1 Satumba 2022 - 20:14
Islamic Jihad : Kulla Alaka Tsakanin Isra’ila Da Turkiyya, Kure Ne

Kungiyar gwagwarmayar Falasdina ta Islamis Jihad, ta yi allawadai da sake dawo da alaka tsakanin Turkiyya da kuma Isra’ila.

A watan hira da kamfanin dilancin labaren IRNA na Iran, wakilin kungiyar ta Islamic Jihad a Iran, ya ce dawo da alaka da Turkiyya ta yi da Isra’ila babban kure ne.

Ya ce amsar da muka baiwa shugaban Turkiyya Recep Teyyib Erdogan, ita ce irin wadda ya fada a lokacin da UAE ta shirya daidaita alakarta da ‘yan sahayoniya.

Abu Sharif, Ya kara da cewa ta hanyar kula wannan alaka, Turkiyya ta zama tamakar wata damara ta baiwa Isra’ila tsaro.

A kwanan baya ne dai Isra’ila da Turkiyya suka sanar da dawo da gabadayen alakar dake tsakaninsu tare da musayar jakadu.

Saidai Turkiyya ta sake nanata cewa dawo da alakarta da Isra’ila baya nufin ta juyawa Falasdinu baya ne, hasali ma wata dama ce ta shiga tsakani a rikicin Isra’ila da Falasdinu kai tsaye tare da dukkan bangarorin.

342/